Ciki na Halima Cisse, mai shekara 25, ya ba ƙasar mamaki kuma ya ja hankalin shugabannin kasar. Lokacin da likitoci a watan Maris suka ce Cisse na bukatar kulawa ta musamman, hukumomi sun dauke ta zuwa Morocco, inda a ranar Talata ta haifi ’yan mata biyar da maza hudu ta hanyar tiyatar haihuwa.
Jariran 'yan mata biyar da maza hudu da mahaifiyarsu duk suna cikin koshin lafiya, "in ji ministan kiwon lafiya na Mali, Fanta Siby a cikin wata sanarwa, inda ta kara da cewa za su dawo gida cikin makonni.
Siby ta mika sakon taya murna ga "kungiyoyin likitocin Mali da Maroko, wadanda kwarewarsu ta kasance farin cikin haihuwar cikin luman".
Your browser doesn’t support HTML5
An yi tsammanin Cisse za ta haifi 'yan bakwai ne, a cewar hasashen da aka gudanar a kasashen Morocco da Mali wadanda suka ce hoton cikin bai gano jarirai biyu ba.
Ba safai a ke samun matan da su ke nasarar ɗaukar yan bakwai ba balle kuma a ce ‘ya ya tara.
Kakakin ma’aikatar lafiya Rachid Koudhari ya ce ba shi da masaniya game da irin wannan haihuwar da yawa da aka yi a daya daga cikin asibitocin kasar, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP.
Karin bayani akan: Mali, da Morocco.