A jihar Bauchi, mutane sama da dubu goma sha biyar ne suka amfana daga shirin samar da ayyukan lafiya kyauta,wanda kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriya, Yakubu Dogara ya dauki nauyinsa.
An gudanardsa ayyukan lafiya iri daban daban da suka hada da tiyata, gwaje gwaje ko auna lafiya, da kuma raba magunguna da bada tabarau ga masu matsalar ido.
An gudanar da aiyukan lafiyar ne a harabar asibitin koyarwa, jami’ar tafawa Balewa dake Bauchi, inda marasa lafiya daga yankunan kananan hukumomi guda ashiri dake jihar suka halarta.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da wanna tallafi sun yabawa wannan gagarumi kokarin da kakakin majalisar wakilan Najeriya ya bada.
Dr. Joseph Haruna Kibo, wanda ya jagoranci likitocin da suka gudanar da aiyukan lafiyan yace sun gudanar da wani babban tiyata inda suka raba wasu tagwaye wadanda suke manne da juna, dayar ta mutu, kudin wanna fida kawai da biya zasu yi da ya kai Naira miliyan biyu.
Facebook Forum