PLATEAU, NIGERIA - Kotun ta kuma soke zaben mamba mai wakiltar Bassa da Jos ta Arewa, a Majalisar Wakilan Najeriya, Musa Agah wanda shi ma ‘dan jami'iyyar PDP ne.
Alkalin kotun, mai shari'a, Elfrida Williams Daudu ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta gudanar da zaben 'yan Majalisun cikin kwanaki casa'in.
Mr. Friday Derwam, ‘dan jarida dake daukar rahotannin shari'u ma gidan rediyo da talabijin mallakar jihar Filato, ya halarci zaman kotun a Abuja ya kuma yi karin haske kan abin da ya wakana a kotun inda ya tabbatar da cewa, kotun daukaka karar ta soke zaben 'yan majalisun biyu bisa hujjar cewa hukumar zabe ba ta yi daidai ba wajen ayyana su a matsayin wadanda suka ci zaben, saboda tun farko jami'iyyar PDP ba ta bi umurnin wata babbar kotu a jihar Filato, na cewa ta yi zaben shugabannin jami'iyya kafin lokacin yin zaben fidda gwani ba.
Da yake tsokaci kan shari'ar, lauya mai zaman kansa dake Sudan Chambers a Kontagora jihar Neja, Barista Isyaku Barau, ya ce alkalin da ta yanke hukuncin ta bai wa dukkan jam'iyyu damar shiga zaben da hukumar zabe zata shirya, ciki har da jami'iyyar PDP da aka soke zaben 'ya'yan nata.
Kotun daukaka karar dai ita ce kutun karshe da 'yan majalisu za su kai kara.
Yanzu dai za a jira ranar da hakumar zabe mai zaman kanta ta kasa za ta sanya ne don gudanar da zabubbukan.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5