Wata Kotu A Nijar Ta Bada Belin Hama Amadou

Shugaban ‘Yan Adawa A Nijar Hama Ahmadou.

Wato kotu a jamhuriyar Nijar ta ba da belin madugun ‘yan adawa Hama Amadou bayan da ya gabatar da kansa a gaban hukumomi sa’oi kadan da komawarsa gida bayan shafe shekaru biyu ya na gudun hijira a kasashen waje.

NIAMEY, NIGER - Tsohon Firai Minista Hama Amadou wanda ainihi daga gidan yari ne ya sami izinin zuwa ganin likitansa a kasar Faransa a watan Afrilun 2021, dawowarsa gida Nijar ke da wuya bai bata lokaci ba wajen gabatar da kansa gaban alkali domin ya yi bayani kamar yadda lauyansa Maitre Mossi Boubacar ya bayyana a hirar shi da Muryar Amurka.

Ya ce da ya dawo ya amsa tambayoyin alkali kuma sun shigar da bukatar a yi masa sakin talala, haka kuma an amince da wannan bukata kamar yadda aka yi wa saura.

“Ina tabbata maku cewa an yi masa sakin talala saboda haka a jiya ya yi kwanansa na farko a cikin iyalinsa. An bi dukkan ka’idodin da ya kamata domin ya bayyana gaban alkali mai bincike. Da ma doka ta ce ana iya gabatar da bukatar ba da beli a duk lokacin da ake so haka kuma aka yi. A karshe an yi masa sakin talala."

A cikin daren Litinin din da ta gabata zuwa wayewar Talata ne Madugun ‘yan hamayya Shugaban jam’iyar Moden Lumana Hama Amdou ya sauka birnin Yamai bayan gudun hijirar na shekaru biyu a kasashen waje.

La’akari da sabon yanayin siyasar da aka shiga a Nijar tun ranar 26 ga watan Yuli ya sa wasu manazarta ke fassara dawowarsa gida tamkar wani matakin share fagen shirye-shiryen zabubukan da gwamnatin rikon kwarya za ta shirya a gaba ne, ko da yake matsalolin da ya yi fama da su a baya na iya zama wata damuwa, da ka iya hana masa shiga wannan fafatawa.

Ta wannan dalilin ne ma ya bukaci magoya bayansa da su zabi ‘dan takarar ‘yan adawa Mahaman Ousman a zagayen farko na zaben shugaban kasa a watan Disambar 2020 da zagaye na biyu da ya gudana a Fabrairun 2021.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kotu A Nijar Ta Baiwa Hama Amadou Baili Bayan Ya Mika Kansa.MP3