Wata Iska Mai Karfi Ta Jefa Miliyoyin Mutane Cikin Duhu A Nan Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump

Iskar da ba'a taba yin irinta ba cikin shekaru 30 a nan Amurka ta jefa miliyoyin mutane cikin duhu a yankin arewa maso gabashin kasar kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane tare da lalata gidaje da dama

Sama da mutane miliyan daya ne har yanzu suke zaune cikin duhu a saboda rashin wutar lantarki a wasu sassa na nan yankin arewa maso gabashin Amurka, yayin da ma'aikata ke aiki ba dare ba rana domin gyara barnar da ta biyo bayan wata iska mai karfin gaske da ta shafi yankin kwanaki uku da suka wuce a yau litinin.

Babu alamar iska ko hadiri jiya lahadi a duk fadin yankunan da wannan iska ta shafa, wadda kuma ta kashe mutane 9, cikinsu har da wasu yara kanana su biyu da bishiyoyi suka fado musu a ka. Amma garuruwa da yankuna da dama su na fuskantar kalubale babba wajen maido da wutar lantarki da kuma kwashe sharar da wannan iska mai kama da mahaukaciyar guguwa ta jibga a yankunansu.

Dubban ma'aikata na musammam ne suka yi ta aiki ba dare ba rana a tsawon karshen makon nan a garuruwan da suka kama daga jihar Virginia a kudu har zuwa Jihar maine a can kuryar arewa.

Har zuwa tsakiyar rana jiya Lahadi sama da mutane dubu 180 suke cikin duhu a Massachussetts, kana sama da dubu 230 a Pennysyvania, yayin da wasu sassa masu yawa suke zaune babu wutar lantarki a jihohin New York, New Jersey, Virginia da Maryland.