Wasu 'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Cocin Owo Sun Shiga Hannu

Janar Lucky Irabor

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce an sake damko karin wasu yan ta'adda guda biyu dake cikin maharan da suka kai harin cocin Owo

An dai kame karin yan ta'addan ne a Omialarafa da ke karamar hukumar Ose a jihar Ondo. 'Yan ta'addan da aka kama sun hada da Al-Qasim Idriss, da Abdulhalim Idriss, Shi Abdulhalim kamar yadda rundunar tsaron tayi karin bayani shine wanda ya kitsa tare da jagorantar wani mummunan hari kan wani sansanin sojoji a jihar Kogi da ya yi sanadin hassarar rayuka,,,

Mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo janaral Jimmy Akpor ya bayyana cewa, jami'an tsaron kasar sun cafke karin 'yan ta'adda biyu da ke cikin gungun maharan nan da suka hallaka gomman masu ibada a majami'ar Saint Francis da ke Owo.

Janar Akpor yace, yan sa'o'i kadan bayan da babban hafsan tsaron kasar Janar Irabor ya bayyana cafke yan ta'adda hudu na farko a jiya, hadin gwiwar sojoji da jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kuma sake damke karin 'yan ta'adda biyu cikin maharan.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Cocin Owo Sun Shiga Hannu

Ku Duba Wannan Ma Shugaban Darikar ECWA Ya Bukaci Hukumomi Su Gudanar Da Kyakkyawan Bincike Kan Kisan Owo