YAOUNDÉ, CAMEROON- Ƙasar Kamaru na ɗauke da gidajen jarida fiye da 600. Daga manyan jaridun da suka fi ɗaukar hankali har zuwa mashiririta masu yadda su ka ga dama. Amma dukkansu suna fuskantar matsala guda daya, wato rashin biyan albashin 'yan jarida yadda ya kamata.
Wannan matsala ce da tambaya akanta ta kasance tamkar haramun. ‘Yan jaridan da kansu suna kiyaye bayar da amsa domin gudun abin da zai iya biyowa baya.
Amma mun ziyarta a birnin Yaounde, a wani gidan rediyo inda ‘dan jarida Alphonse ya yanke shawarar yin magana. Wannan ‘dan jarida mai shekaru 52 ya bar gidan jaridar da ya yi aiki har shekarar da ta gabata. Ya bukaci maigidan nasa da ya biya shi albashin watanni 21, wanda ya ja zuwa hukumar kula da ma'aikata.
Alphonse ya ce “na yi aiki na tsawon shekaru fiye da 20. Tsohon Maigida na ya ci mini kimamin albashi na watanni 22. Da na kai ƙaranshi wurin hukumar kula da ma'aikata, abin da aka biya ni bai fi albashin wata 7 ba, alhalin na yi aiki a matsayin magatakardan wannan kamfani na tsawon shekaru 11, albashin kuma bai fi jaka 150 da ake bani ba”
Albashin jaka 150, wato dala 250. A hakan kuma babu wani tattali da ake yi wa ‘yan jaridan wajen tsara rayuwa bayan ritaya. SNJC, kungiyar 'yan jarida ta Kamaru ta yi Allah wadai da wannan matsalar.
A wannan rana, shugabar kungiyar Marion Obam tare da abokin aikinta sun yi la'akari da yanayin rashin biyan albashi a wannan sana'a. Ga ƙungiyar, rashin jin daɗin ‘ƴan jarida da ba a biyan su albashi, shi ya sa su zama masu jarabtuwa ga cin hanci da rashawa.
Daga cikin jaridun da aka lissafa wajen rashin biyan albashi, akwai sananniyar jarida mai suna "Le Jour" ta Haman Mana. Wannan darektan ya amince da cewar akwai jinkirin albashi, sai dai ya ɗora alhakin kan matsaloli da suke fuskanta na cikin gida da kuma kusan fatara.
Hamman ya ce “lallai kuwa ana kukan rashin biyan albashin ‘yan jarida, amma ba a duba sauran basussuka da suke kan mu wajen sayan takardu da ɗaukar sauran nauyi da muke yi”
Duk da tallafin da gwamnati ke bayarwa, wanna rikicin albashin na ‘yan Jarida ya kasa ƙarewa.
Saurari cikakken rahoto daga Mohamed Bachir Ladan:
Your browser doesn’t support HTML5