YAOUNDE, CAMEROON - A cikin Makon da ya gabata ne Bataliyar rundunar ‘yan sanda ta gaggawa da ake kira BIR a takaice ta kai samamen da ya yi sanadiyyar kisan jagoran 'yan a-waren da ake yi wa lakabi da Field Marshall a mararrabar Kumba, lamarin da ya jawo hankalin mutane da yawa cikin dan lokaci. An yada hotunan gawar Field Marshall a cikin wata mota kewaye da sojoji a kafafen sada zumunta.
An jima ana neman Marshall bisa laifin cin zarafin da ya yi wa sojoji, hukumomi da mazauna yankin Lebialem a jihar Kudu maso yamma. Bayan bai wa sojojin wahala tsawon watanni, hukumomi sun ce wannan nasara ce da ta nuna gagarumin sauyi a ma'aunin karfin da ‘yan a-waren ke da shi a yakin.
"Tun da har kuka ga mun samu nasarar gamawa da Field Marshall, kuma kun tabbatar da hakan, ku sani cewa akwai sauran jiga-jigan ‘yan a ware irinsu "No Pity" da "Ten Kobo" da ake nema, kuma a matsayina na wakilin Shugaban ƙasa, da Ministoci, da Firai Minista a nan sashen, ina tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a kawar da dukkansu," in ji shugaban yankin Mémé Chamberlin Ntou'ou Ndong.
Mazauna Lebialem sun ce sun sami kwanciyar hankali kuma za su iya komawa gidajensu yanzu.
“Muna gode wa Allah! Wannan mutumin da aka kashe ya tsoratar da mu sosai a nan. Wani lokacin da dare za ku ji suna harbe harben bindiga haka nan. Don haka muna godiya ga sojojin nan da suka dawo mana da ɗan zaman lafiya," a cewar wani mazaunin Kumba da ya bayyana sunasa a matsayin Mister Peter.
Sai dai mutuwar Field Marshall ba tana nufin kawo karshen rikici a yankin Ingilishin Kamaru ba.
Suleman Mohammed, manazarcin harkokin siyasa ne, ya ce mafita daya ce a wannan rikicin, ya kamata a hau teburin sulhu da 'yan a-waren ba a kashe ba. Saboda mutuwar Field Marshal ba zata sauya lamarin ba domin yaran Amba na nan tafe. "
Tun a shekarar 2016 ne dai aka fara rikicin yankin. Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway (NRC) ta bayyana cewa rikicin na yankin Anglophone na ɗaya daga cikin rikice-rikicen da aka yi watsi da su a duniya wanda ya yi sanadiyyar tilastawa mutane sama da 60,000 yin gudun hijira zuwa makwabciyar kasar Najeriya wasu fiye da 700,000 kuma suka rasa matsugunansu.
Saurari rahoton Mohammad Bachir Ladan daga Yaoundé: