Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan Jabu Na Ci Gaba Da Janyo Asara Ga Gwmanatin Kasar Kamaru


Kayan Jabu A Kasar Kamaru
Kayan Jabu A Kasar Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta na asarar Biliyan 100 na kudin CFA kowace shekara a sanadiyar kayan jabu da suke shigowa kasar.

YAOUNDÉ, CAMEROON - Kayan jabu du ns dsmun karbuwa da kuma kasuwa a rayuwar yau da kullun na masu amfani da kayan masarufi daban daban a kasar Kamaru da ya ya ke zama da kyar akan iya bambanta kayayyaki masu kyau da jabu. Bayan hakan yana gurbata tattalin arzikin kasa, yana kuma kawo yawan illoli a lafiyar masu amfani da su. Duk matakai da gwamnati ta dauka basu magance wannan matsalar ba.

Alice Maguedjio, shugabar kungiyar ‘yan kasuwa na yankin Wouri ta ce hakika, bincike ya nuna cewa da ‘yan kasuwa basu saro jabu ba, mai saya ma ba zai yi amfani da shi ba. Sanin haɗarin wadannan kayayyaki a kiwon lafiya ya karfafa yunƙurin wayar da kan jama'a da ƙarfafa ‘ƴan kasuwa kan gaskiya.

Bisa kididdigar da hukuma ta yi, kayan jabun na sa kasar Kamaru ta yi asarar sama da biliyan 100 na CFA a kudaden haraji a kowace shekara. Babu wani yanki na kasar da ya tsira.

Kwararrun masana suna ba da shawarar samun kayayyaki daga kamfanoni kai tsaye domin gudun sayen jebu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Bachir Ladan:

Yin Jabu Na Ci Gaba Da Janyo Asara Ga Gwmanatin Kasar Kamaru
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG