Bayanai dai sun nuna cewa a cikin makon jiya ne mutanen cikin kayan sojoji su ka yi awon gaba da shugaban Fulanin na jihar Kogin Alh.Wakili Damana daga gidansa daga cikin karamar hukumar Lokoja a cewar Sakataren Kungiyar Miyatti Allah na Jihar Malam Adamu Abubakar.
Rundunar Yan sanda ta jihar Kogin dai tace tana gudanar da bincike akan lamarin.
A hirar shi da Sashen Hausa, kwamishinan "yan sanda na jihar Kogi, Mr Ede Ayuba, ya ce a gaban mutanensa aka wuce da shi kuma shi kanshi ya kira lambar Shugaban Fulanin kusan sau biyu ko sau uku amma tana kara ba’a daga ba. Ya kuma bayyana cewa, suna kan bincike sosai domin gano ina ne ya ke.
Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Kogin ke fafutukar ganin ta kubutar da Shugaban Karamar Hukumar Yagba da ke hannun 'yan bindigar bayan da suka hallaka wani kwamishina na ma’aikatar fanshon jihar a karshen makon da ya gabata, inji kwamishinan labarai na jihar Mr. Kensly Panwo.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5