Rahotanni daga jihar Kogin Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Yagba West Pius Kolawole.
Bayanai sun yi nuni da cewa Solomon, na komawa gida ne daga Ilorin zuwa Kabba sai wasu ‘yan bindiga suka budewa motarsu wuta.
A cikin motar har da shugaban hukumar fansho na jihar, Adebayo Solomon wanda ya rasa ransa sanadiyyar bude wutar da ‘yan bindigar suka yi.
Lamarin ya faru ne wasu ‘yan kilomitoci daga kauyen kira Eruku da ke kan iyaka da jihar Kwara da yammacin ranar Asabar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Kogi DSP William Aya da Muryar Amurka ta nema don jin karin bayani, ya ce a ba shi lokaci zai waiwaye mu ba da jimawa ba.
Amma kafofin yada labarai da dama sun ce rundunar ta tabbatar da aukuwar lamarin tana mai cewa, da Kolawole wanda aka fi sani da Akeweje da Solomon, suna tafiya a mota guda ne a lokacin da maharan suka far musu.
Rahotanni sun ce an baza jami’an tsaro a yankin da harin ya faru domin ganin an ceto shugaban hukumar Kolawole.
Karin bayani akan: jihar Kogi, Edo, Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako guda, bayan da aka kai wani hari akan Sanata Clifford Ordia da ke wakiltar mazabar Edo Central a majalisar dokokin Najeriya a yankin jihar ta Kogi.
Yankuna da dama na jihar wacce ba ta da nisa da Abuja, babban birnin Najeriya, sun shiga kangin masu garkuwa da mutane.
Ko a watan Janairun bana, sai da wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan kasuwar kantin kwari 18 a yankin na jihar Kogi, a lokacin suna kan hanyarsu ta zuwa garin Aba domin sayo kayayyaki.
Amma an sako su daga baya, bayan da aka biya kudin fansa kamar yadda rahotanni suka nuna.