Bayanai dai sun nuna cewa an tsinci gawar Nelson Achukwu mai lalurar na kasa, bayan da wasu danginsa sun biya kudin fansa akallah Nera Milliyan 15.
Rundunar yan sadan jahar Anambra ta tambatar da faruwa lamarin a wata hira da Muryar Amurka.
CSP Geofrey Ogbonnaya shine mai Magana da yawun rundunar yan sanda jahar kuma ya ce "rundunar 'yan sanda jahar Anambra tsaye take yayin da ta samu wannan labarin. Haka kuma muna gudanar da wani sintiri na hadin gwiwa tare da sauran jami’an tsaro domin ganin mun kamo wadanda suka aikata wannan mumunan laifi."
Wanan dai shine karo na hudu da 'yan bindiga suka cire kan 'yan siyasa ko jami’an tsaro a jahar ta Anambra.
Masu sharhi kan harkokin tsaro na ci gaba da bayyana shankun su game da batun tsaro a kasa.
Ku Duba Wannan Ma IPOB Ta Nesanta Kanta Da Kisan Sojojin Najeriya Da Ke Shirin Yin AureDakta Bala Sale mai sharhi kan harkokin tsaro yace abin taikaici shine ita gwamnati bata so ace ta gaza wajen harkan tsaro ko da yaushe suka fito sai suce suna kokarinsu.
A watan Mayu da ya gabata wasu 'yan bidinga sun sace tare da datse kan wani dan majalisa Hon. Okechukwu Okoye suka kuma halaka wani sojan Najeriya mai suna Linus Musa Audu da Amaryan sa, yayin da suke shirin aure a jahar Imo.
Haka kuma anyi kasan gilla ga wata matar aure mai suna Huraira da 'ya'yan ta hudu da basu jiba basu gani ba a jahar Anambra.
Kashe kashen gilla dai a yankin kudu maso gabashin Najeriya ya shiga daukan sabon salo yayin da Najeriya ke fuskanta babban zaben kasa na shekara ta 2023.
Saurari cikakken rahoton Abubakar Lamido Sakkwato cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5