Rundunar sojin Najeriya, ta zargi kungiyar IPOB da ke rajin ballewa daga kasar, don kafa Biafra da fille kan sojojinta biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa bikin aurensu a kudancin kasar.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar dauke da sa hannun kakakinta Birgediya- Janar- Onyema Nwachukwu, rundunar ta kwatanta kisan Master Warrant Officer, Audu M. Linus (ritaya) da Gloria Matthew a matsayin “tsananin rashin imani.”
Linus da Gloria na hanyarsu ta zuw ajihar Imo ne domin halartar bikin aurensu na gargajiyarsu.
“Wannan mummunan aika-aika da ke yawan faruwa, ya nuna karara irin kiyayyar da rashin da’a da rashin bin doka da ‘yan kungiyar ta IPOB/ESN suke nunawa tare da muzgunawa al’umomin Igbo.” Sanarwar ta Nwachkwu ta ce.
Lamarin dai ya faru ne a ranar 30 ga watan Afrilun 2022.
Sai dai tuni kungiyar ta IPOB ta nesanta kanta wannan lamarin inda ta ce ta yi mamaki da sojojin kasar suka danganta laamrin da su.
“Muna zargin sun yi haka ne, domin bata sunan kungiyar a idon duniya, mu ba mu san komai dangane da kisan sojojin ba.” Daya daga cikin kusoshin kungiyar ta IPOB Chinanzo Nwachukwu ya fadawa Muryar Amurka.
Da aka tambaye shi ko wa yake ganin sun yi kisan, sai ya ce, wannan tambaya ce da za a yi wa gwamnan jihar, domin tsaron jihar a hannunsa ya ke.
Ita dai rundunar sojin ta Najeriya ta sha alwashin zakolu wadanda ke da hannun a wannan aika-aika tare da hukunta su.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar Sokoto daga Fatakwal: