Dr. Keti Namala wani malamin jami'ar Adamawa yace muhawara ce ta tona asiri daga bangarorin biyu.
Dr. Namala yace su 'yan takarar suna fadawa Amurkawa ne abubuwan da suke son su ji ba wai abun dake zukatansu ba. Kamar Clinton tace akwai abun da take gayawa mutane amma kuma akwai abun dake zuciyarta.
Abdullahi Adamu tsohon kwamishanan yada labaru na jihar cewa yayi idan aka yi la'akari da muhawara ta farko da ma ta baya bayan nan Amurkawa suna nunawa duniya cewa son da suke yiwa mutum ba ta ido rufe ne ba. Suna son su san abubuwan da zasu yiwa kasar ne da zai anfani kowa da kowa.Yace har maganar biyan haraji ma ta taso.
Muhawara ta biyu ta sake sa har yanzu Hillary Clinton tana gaban shi Trump a ra'ayin masu jefa kuri'a. Saboda haka soyayyar Amurkawa ta ta'allaka ne akan abun da ka yiwa kasa da can da kuma zaka yi idan ka zama shugaba.
Shi ma Abdullahi Abdulmummuni tsohon dan majalisar jihar Adamawa yace sun ga muguwar rawa tsakanin Trump da Clinton musamman akan batun cancanta. Hillary ta kalubaleshi akan rashin biyan haraji sabanin abun da ita tayi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5