Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Trump Ya Zama Shugaban Amurka Zai Haddasa Yaki - Hirse


Trump da Clinton
Trump da Clinton

A zantawar da yayi da Muryar Amurka Jakada Bagudu Hirse yace duk abun da ya shafi Amurka ya shafi duniya gaba daya domin Amurka wadda ba zata zama tsibiri ba tana muamala da duniya saboda haka Donald Trump idan har ya samu shugabancin kasar zai haddasa yakin duniya.

Dole Amurka tayi cudanya da sauran kasashen duniya domin ba zata taba zama wata tsibiri ba da ta ware kanta.

Yace Donald Trump na son ya sa Amurka ta zama tsibiri bisa ga furucinsa, wato ya yanke kasar daga sauran kasashen duniya. Da jin lafazinsa da maganganun da yake yi idan ya zama shugaban Amurka zai kawo yakin duniya na ukku.

Da aka fada ma shi Jakada Hirse cewa wasu kalamun Trump siyasa ce kawai domin yana yinsu ne ya samu goyon bayan wasu amurkawa da suka fusata da wasu manufofin gwamnatin yanzu, sai yace shi bai gani haka ba dalili ke nan yake rokon Allah ya ba Hillary Clinton nasara ta zama mace ta farko da zata zama shugabar Amurka.

Akan cewa wasu na ganin manufofin Clinton akan zamantakewa suna gurbatata sai Hirse yace ai mutum dan tara ne. Babu wanda ya cika. La'anin dake tattare da Trump ya fi na Clinton. Yace an sami Trump da laifuka da yawa.

Kan abun koyi da Amurka yace kodayake Najeriya na bin irin tafarkin Amurka amma a Najeriya akwai munafunci da karya. Fatansa shi ne Allah ya sa masu aiki da Buhari zasu aikata gaskiya kamar yadda shi Buharin mai aikata gaskiya ne.

Ga firar da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG