Wasu Tagwaye Da Aka Sace, Aka Kuma Sayar Sun Hadu A TICTOK

Tagwayen da aka sace, suka hadu a TİK TOK

Wasu tagwaye waɗanda aka sace, aka raba kumasu, aka kuma siyar da su tun suna jarirai sun sake haduwa bayan daya daga cikinsu ta gane ‘yaruwarta a cikin wani bidiyon TikTok.

WASHINGTON, D. C. - An haifi Amy da Ano a jihar Georgia a shekara ta 2002, amma an sace su daga hannun mahaifiyarsu kuma aka sayar da su a kasuwar yara ta haramtacciyar hanya. A lokacin aka gaya wa mahaifiyarsu Aza cewa 'ya'yanta sun mutu.

Tagwayen da suka hadu a TİK TOK

Ɗaya daga cikin tagwayen, Amy Khvitia, ta gane 'yar'uwarta mai shekaru 12 lokacin da ta fito a wani bangare na shirin Georgia Got Talent. Dayar kuma, Ano Sartania, ta shiga shakku bayan shekaru bakwai lokacin da wata kawarta ta aiko mata da bidiyon Amy na TikTok kuma ta lura suna kama matuka da juna.

Tuni dai yaran suka hada kansu bayan da wani abokinsu ya hada su a Facebook, kuma sun gano cewa wata kungiyar fataucin kananan yara ta Georgia ce ta raba su, wanda ke sayar da jarirai tun daga farkon shekarun 1950 zuwa 2005.