A India kotun kolin kasar tana duba dokokin Musulunci kan saki da zamantakewa, dokoki da suka baiwa maza damar ambatar kalmar "talaq" watau saki har sau uku. Matakin da kotun take dauka ya biyo bayan karar da wata mace musulma ta shigar tana kalubale kan damar saki lokaci daya, da kuma matsayar auren mace fiyeda daya.
Amma fa kungiyoyin musulmi masu ra'ayin mazan jiya suna bayyana matukar adawa da duk wani kokarin da kotun zata yi na gudanar da bincike kan dokokin addini da suka shafi iyali da makamantansu.
Wata musulma mai suna Shayara Bano, wacce mijinta ya saketa bayan shekaru 13 suna tare ta hanyar saki uku lokaci guda. Tace wannan sharadi ya maida mata tamkar wata mallaka shigen kaya ga maza. wanda a ganinta hakan ya saba da zaman yau na mutunta 'yancin Bil'Adama, da kallon duka jinsunan biyu a zaman daya babu wanda ya fi wani.
A cikin karar, Bano tace, akwai mazaje da suka saki matansu ta aike musu sakonni ta dandalin FaceBook, ko ta Skype, ko kuma ta sakon text.