Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Ba'ayi Sa'a Ba Kasar Amurka Baza Taje Gasar Cin Kofin Duniya Ba


Koch na kungiyar ‘yan wasan kwallon kafar kasar Amurka, Jurgen Klinsmann, yayi wasu kalamai marasa dadi, bayan wasan da suka buga a kasar Guatemala, ta yankin kudanci kasar. An dai tashi da ci 2-0 da babu a ranar Juma’a, yanzu haka dai kasar ta Amurka nada damar mintoci 90, su kokarta wajen ganin sun samu makin da ya kamata don zama cikin jerin zakaru.

A cikin jerin wasan da ake bugawa na zakaru don samun shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2018, da ake sa ran za’a buga a kasar Rasha. Tun dai a shekarar 1990, rabon da a cire kasar Amurka, kamin kaiwa cikin jerin kasashe da zasu buga wasan gasar cin kofin duniya. Amma a yanzu haka dai idan kasar ba tayi kokari ba, a wasan da zasu buga a ranar Talata mai zuwa ba, ba zasu samu damar zuwa gasar cin kofin duniya ba.

Irin nasarori da kasar ke samu a duk bayan shekaru 4, na taka rawar gani, wani abun dubawa ne wanda yanzu haka kasar tana kangaba a kusan komai a duniya, amma sai gashi a wasan kwallo tana neman shan kunya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG