A wasu lokkuta mutane kanyi maganar masoyan su musamman da abokan su, babu ma kamar idan mace ko namiji naso su kururuta gwanayen su. Hakan na da matukar hadari idan ba’a kula ba. Babban sirrin soyayya mai nagarta shine, kada mace ko namiji su dinga bayyanar da yadda soyayyar su ke gudana da masoyan su da abokan su.
Muddun mace ko namiji zasu cika magana akan wasu abubuwa masu kyau dangane da masoyan su da kawayen su, to watarana kuwa zasu sha mamaki. Domin kuwa abun nan da ake cewa abincin wani gubarwani, kan hau kansu. Haka masoya su kokarta boye duk wasu sirrin su a tsakanin su da abokan su, kada mace ta dinga fada ma kawayen ta inda saurayin ta yake aiki ko nawa albashin shi yake koda ta kaiga sanin hakan.
Ba kuma kowace irin magana ya kamata ace mata ko samari nayi da abokan su dangane da masoyan su ba, domin kuwa wasu sirrikan da mutun ya bayyana ma abokin, kan iya zama makasa gare shi a wajen budurwar ko saurayin. Sukan iya amfani da wannan ga ainihin wanda akeyi don shi. Don su kwace soyayyar ta dawon kansu, don sun san abun da wannan mutumin yake so, sai suyi mishi. Kuma wasu kan yi amfani da wannan damar wajen ganin sun lalata danganta tsakanin masoya sai su su shige.