Kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona ta ba kungiyar Real Madrid ratar maki 10 a teburin wasannin lig-lig na Spain, La Liga, yayin da kungiyoyin biyu ke shirin karawa a ranar asabar din nan. A koyaushe wadannan kungiyoyi biyu suka gwabza, akan kira wannan ruguntsumi nasu da sunan El Classico, saboda irin tsama da gasar dake tsakaninsu tsawon shekaru aru aru.
A watan Nuwamba, FC Barcelona ta bi Real Madrid har gida ta lallasa ta da ci 4 da babu, inda Luis Suarez ya jefa kwallaye biyu yayin da Neymar da Andres Iniesta suka jefa sauran kwallayen biyu.
Sai dai kuma a wannan karon, Sergio Ramos, ya bayyana kwarin guiwar cewa zasu dauki fansa idan sun ziyarci FC Barcelona a filinta na Camp Nou jibi asabar.
Yau kusan shekaru hudu ke nan Ramos da kungiyarsa ta Real Madrid ba su samu nasarar ko da wasan kwallo guda a filin na Camp Nou ba, amma dan wasan yace yana da kwarin guiwar kungiyarsa zata farfado ta bada mamaki.
A bayan karawarsu ta El Classico ta farko da ba ta yi dadi a bana ba, Ramos ya fadawa gidan telebijin na Real Madrid cewa zasu yi tattaki da kwarin guiwa da kuma kudurin kwace dukkan maki uku na wasan domin rage gibin dake tsakaninsu na yawan maki a teburin La Liga.
Real Madrid tana matsayi na uku a teburin La Liga, maki 10 a bayan FC Barcelona da take ta daya. Wasanni 8 kawai suka rage kafin a kammala kakar kwallon lig ta bana a kasar Spain.