''Sojojin rundunar kawancen yankin tafkin Tchadin sun kuma dakile wani farmakin Boko Haram a garin Kwatan Turare kusa da Baga, inda bayan hallaka 'yan ta'addan, dakarun sun kuma samo Roka da gurneti da bama bamai guda bakwai, jiragen ruwa da harsasai kana soja daya ya rasa ransa yayin wannan artabu.''
MNJTF NAJERIYA
Daga bangaren Tarayyar Najeriya , dakarun na MNJTF ko FMM da ke shiyya ta uku wato sector 3 mai sansani a Monguno jihar Borno, sojojin sun yi wata fafatawa mai zafi da 'yan ta'addan da suka yi yunkurin kutsawa yankin, inda bayan musayar wuta mai zafi 'yan ta'addan suka ja da baya, yayin kuma da dakarun suka bisu inda suka hallakasu kana suka samo makamansu.
Dakarun kazalika sun kuma ceto wasu yara guda biyar da 'yan ta'addan suka sace lokacin da yaran suka fita neman kirare, sannan an samo sabbin babura kirar BOXER guda biyar da 'yan ta'addan ke amfani dasu a tsibirin tafkin Tchadin.
MNJTF NIJAR
Can daga bangaren jamhuriyar Nijar kuwa, dakarun yankin tafkin Tchadin dake shiyya ta uku mai sansani a jihar Diffa yayin da suke sintiri akan hanyar KARA zuwa DIFFA sun cafke wasu abokan burmin 'yan ta'adda guda hudu dauke da litar mai dubu daya zasu kaiwa 'yan ta'addan a cikin daji.
Sun dai boye man ne a cikin jakunkunan roba a wata mota mai kirar JEEP TOYOTA HIGHLANDER mai dauke da lambar jihar Yoben Najeriya.
An dai dauko man ne daga garin kan iyaka na Maine Soroa ta Nijar e zuwa ga 'yan Boko Haram a yankin tafkin Tchadin, kana sojin sun kuma samu tsabar kudi har Naira dubu dari shida da hamsin daga miyagun.
MNJTF KAMARU
Kawo yanzu kimanin manyan mayakan Boko Haram su saba'in ne suka yi saranda a jiya kana suka mika wuya ga dakarun MNJTF na Kamaru da kuma a Jamhuriyar Nijar kamar yadda kakakin dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadin Laftanar Kanar Ademola Adegoke ya sanar.
Kanar Adegoke ya ce a daukar bayanan mayakan da suka yi sarandar yayin da ake mu'amalantarsu daidai da yadda tanade tanade da dokokin kasashen duniya suka tanadar kan duk wani dan ta'addan da ya mika wuya don radin kansa, Babban kwamandan dakarun kasashen yankin tafkin Tchadin, Janaral AK Ibrahim ya hori dakarun da su kara jan damara da jajircewa wajen kara tunkarar 'yan ta'addan har sai an kawo karshensu baki daya.