An gurfanar da wasu matasa 6 shida a kotun Magistire dake Ebute Meta a Jihar Legas, bayan kama su da laifin tsafi, bayan sun dandake kan wani fasto da wasu ‘yan uwan sa da dutsen nika.
Waddanda ake zargin wato Chibozor Igwe mai shekaru 19, da Omotayo Onamoyegun, 25, Samuel Ameze, 38, Gift Ameze, 35, Fatai Adebaye a.k.a Alashe, 34, da wani matsafi.
Suna fuskantar caje-caje bakwai da suka shafi makirci, kisa da sata.
Mr. Emmanuel Eze, wani lauya daga bangaren binciken manyan laiffufuka, Panti, daga jihar, ya bukaci kotu ta ajiye waddanda ake zargin a gidan yari kuma ya bukaci kotun ta aika da litafin laifukan zuwa hukumar saurarren kararraki.
Eze ya ce waddanda ake zargin sun aikata wannan laifin ne ranar 26 a watan Nuwambar bara, a yankin Ofin, a wani wuri mai adreshi lamba 12, Alajo close, da Abule Oshorun, Ibeshe a Ikorodu.
Mai shari’a Mrs Bola Folarin- Williams, ta yanke hukuncin daure masu laifin a gidan yarin Ikoyi, yayin da ake jiran shawarar ofishin darakatan hukumar saurarren kararraki.