Masu bincike sun gano Jigidar Halittar dan’adam ta DNA a jikin wani kwarangwal da ya kwashe shekaru 10,000 a wani kogo, mai tsatson bakaken mutane da kuma kalar ido tsanwa.
Masu bincike na tsangayar gidan ajiyar kayan tarihi da jami’ar College dake Landon, sun bayyana wani kwarangwal mai suna “Chaddar Man” wanda aka tsinta a birnin Cheddar Gorge a yankin kudancin Ingila a shekarar 1903.
Wannan shine kwarangwal mafi tsufa a tarihin duniya da aka samu a kasar ta Birtaniya, mai gudanar da binciken Mr. Ian Barnes, wanda ya dai-daita kwarangwal din ya debo jigidar hallitar daga cikin kurar dake jikin kwarangwal din.
Masu binciken sun tabbatar da cewar mutumin da aka tsainci kwarangwal din nasa, na da tsanwar ido ne, da bakar suma, kana da alamun nau'in fatar jikinsa baka ce. Gidan talabijin na kasar birtaniya zai gabatar da binciken a ranar 18 ga wannan watan.
Facebook Forum