An kirkiri motar farko ta mussamman domin anfani da ita a duniuyar Mars, kuma a yanzu haka tana kan hanya zuwa duniyar wata a cikin kumbo mafi girma da aka taba harbawa zuwa duniyar wata.
Shugaban binciken na SpaceX Mr. Elon Musk, ya tabbatar da sabuwar motar Telsa Roadstar, wadda aka gabatar a gaban mambobin kamfanin Falcon Heavy daga Jihar Florida.
Motar ta kasance mafi karfi a cikin motacin da aka kirkira domin tafiya a sararin samaniya, yayin da ake gwajin tafiyar motar a ranar laraba 7, ga watan fabarairu.
Mr. Musk, ya ce tura moatr da aka yi na karshe don tafiya a sararin samaniya, zata isa takanin duniyar Mars da ta Jupiter, amma shirin ainihi da aka yi shine ba zai wuce duniyar Mars ba.
A wurin zaman direban motar, an saka mutun-mutumi don juya motar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, wanda aka sakama suna Starman.
Sai ya kara da cewar, basu da shirin amfani da wannan motar domin amfanin mutane, amma suna aiki don kirikiro da wata babbar mota da zata yi tafiya a sararin samaniya dauke da mutun.
Facebook Forum