NIAMEY, NIGER - Malam Mansour Ousman, mazaunin birnin Cotonou a jamhuriyar Benin ne, tun a shekarar 2020 ya yi rajista a Nijer da nufin zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali, sai dai bayan shafe makonni biyu a birnin Yamai ya na jiran jirgi ya gano cewa wannan tafiya ba za ta yiwu ba a bana.
Shi ma Mikha’il wanda ya yi sha’awar zuwa Saudiya daga Nijer a maimakon ya yi rajista a jamhuriyar Benin inda ya ke zaune, ya tsinci kansa cikin irin wannan hali.
A tsakiyar makon jiya ne gwamnatin Nijer a ta bakin kakakinta Tidjani Abdoulkadri ta bada tabbacin daukar dukkan matakan ganin kowane daga cikin maniyata 7,194 da suka yi rajista sun isa kasar Saudiya kafin shudewar wa’adin ranar 6 ga watan Yuli, sai dai rashin zuwan babban jirgin Boeing 747 da aka yi hasashen zai fara kwashe mutun sama da 500 a duk sawu daya ya sa aka fara shakka, abinda ya sa wasu maniyatan suka fara tunanin komawa gida don rungumar kaddara.
Bayanai daga sashen kula da harkokin sadarwa a hukumar alhazai ta kasa ta COHO na cewa daga cikin maniyata 7,194 da suka yi rajista 5,107 sun samu tafiya yayin da ake ci gaba da fafutikar ganin sauran maniyata 2,087 da suka rage sun shiga Saudiya tun wuri bai kure ba.
Matsalolin aiyukan Hajji a Nijer wani laifi ne da ake dora alhakinsa a kan ejojin kamfanonin Hajji da Umara saboda yadda wasu daga cikinsu suka mayar da abin kasuwanci kuma a dayan gefen ana zargin hukumar alhazai ta COHO da rashin sanin makamar aiki kamar yadda abin ke shafar kamfanonin shatar jiragen jigilar maniyata.
Saurari rahoton Souley Barma.
Your browser doesn’t support HTML5