Paul Biya ya baiwa alhazai bilayan 1 na CFA a matsayin tallafi bayan jayayya da ta bayyana tsakanin kungiyoyin musulmai da ministan cikin gida dangane da karin kudin zuwa Makkah.
Har ila yau shugaban ƙasa Paul BIYA ya saurari koke-koken musulmin dangane da kammala aikin hajjin a Makkah, daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda 5.
Al'ummar Musulmi wanda a cewar sanarwar manema labarai na ministan cikin gida a ranar 30 ga watan Mayu da ya gabata, dole ne su biya 3.294500f don tafiya aikin hajji. A yanzu sun biya 2.242000f, kamar yadda aka saba.
Karin da aka yi sama da miliyan daya (1.052000f) ya janyo rashin fahimta da ya sa maniyyatan suka nemi goyon bayan shugaban kasa don rarrabewa tsakanin su da Minista Atanga Nji.
Fessal Mounir, janar din kungiyar Assovic yace "Musulman Kasar Kamaru sun yi farin ciki da gaske da wannan tallafawa na shugaban kasa Paul Biya. Inda ya umurci ministan kudi da ya baiwa hukumar kula da aikin hajji biliyan 1 domin daukar nauyin masu zuwa aikin hajjin bana."
Domin kiyaye matsaloli kan wannan kyauta ta shugaban kasa, Fessal Mounir ya yi kira ga hukumar alhazai ta kasa da tayi rabo bisa adalci duba da yadda irin wannan guzuri kan janyo zargi,
Yace"muna kira ga hukumar alhazai da la’akari kan wannan kokari da shugaban kasa yayi. Muna kuma shirye mu kawo namu gudummawa ga ministan cikin gida a matsayin sa na shugaban wannan hukumar idan ya bukaci shawarwarin mu. Baya da haka, muna kira ga sake fasalin hukumar aikin hajji ta kasa domin kiyaye gaba"
Wannan ba shine karo na farko da ake samun matsala tsakanin alhazai da hukumar aikin hajji a kasar kamaru ba. Amma ana fatar zai zamo na karshe.
Saurari cikakken rahoton Mohamed Ladan cikin sauti: