Wasu Kungiyoyin Agaji Da Hadin Gwiwar Adamawa Sun Kirkiro Manhaja Da Zata Inganta Lafiyar Jarirai

Najeriya na daga cikin kasashe masu tasowa dake fama da rashin ingantattun abubuwan kiwon lafiya da hakan ke haifar da yawan mutuwar jarirai da kananan yara musamman 'yan kasa da shekara biyar.

Hakan ya sa kungiyar da ke ba da agaji ta kasa da kasa wato Red Cross da hadin gwiwar cibiyar kiwon lafiya ta al'umma ta "Swiss Tropical" da kuma hukumar lafiya matakin farko ta jihar Adamawa su ka kirkiri wata manhaja da zata taimakawa kananan likitoci wajen dubawa da kuma inganta lafiyar jarirai da kuma yara ‘yan kasa da shekara biyar.

Almanach wato "Algorithm" ta kula da cutukan yara Manhaja ce da za ta maye gurbin hadedden tsarin kula da cutukan yara "IMCI" a takaice da hukumar lafiya ta duniya ta bullo da shi don inganta lafiyar yara.

An fara amfani da manhajar Almanach ne a shekarar 2016 a jihar Adamawa da taimakon Red Cross da kuma Swiss TPH inda a yanzu ne wadannan kungiyoyi zasu mikawa hukumar Lafiya Matakin Farko ta jihar Adamawa wannan manhajar don cigaba da amfani da ita wajen inganta lafiyar yara.

Shugaban hukumar lafiya matakin farko na Jihar Adamawa Dr. Sulaiman Saidu Bashir ya bayyana irin ingancin da su ka samu a amfani da su ke yi da manhajar wajen duba lafiyar yara da kuma irin shirin da su ke yi don ganin amfani da na’urar da kuma manhajar ya dore.

A halin da ake ciki yanzu kimanin yara ‘yan kasa da shekara 5 dubu dari takwas ne ke bukatar kulawa ta kiwon lafiya a Jihar Adamawa.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Kungiyoyin Agaji Sun Hadda Gwiwa Da Adamawa Don Kirkiri Wata Manhaja Da Zata Inganta Lafiyar Jarirai