Wasu Kungiyoyi Sun Fara Ruguguwar Dauko Layvin Kurzawa

Layvin Kurzawa

Kungiyar Tottenham ta sake komawa zawarcin dan wasan gefe na Leicester City Demarai Gray mai shekaru 21da haihuwa tun a shekarar da ta gabata Tottenham suka bukaci sayen dan wasan amman kungiyarsa ta Leicester city ta ki amincewa.

Har ila yau Kocin kungiyar ta Tottenham Mauricio Pochettino na sha'awar ganin ya dauko dan wasan baya na PSG mai suna Layvin Kurzawa, ita ma Chelsea ta nuna sha'awarta ta ganin ta sayi dan wasan.

Kungiyar Lyon da juventus sun jera sahu guda wajan zawarcin dan wasan gaba na Manchester United Anthony Martial, Crystal palace tana duba yuwuwar sayar da dan wasan ta na gaba Christian Benteke, 27, a karshen kakar wasan bana.

Kungiyar Tottenham, tana yunkurin tsawaita kwantirakin dan wasanta Erik Lamela's na tsawon shekara guda zuwa 2020. Dan wasan tsakiya na Napoli Jorginho yana daya daga cikin na gaba gaba wanda Kocin Manchester united Mourinho ya ke nema domin su maye gurbin Paul Pgoba a kungiyar in har dan wasan ya bar kungiyar.

Newcastle united, zata sake tattaunawa da kungiyar Chelsea kan batun sayen dan wasan gefenta Kenedy, 22, a matsayin din-din-din maimakon aro.

Kocin kungiyar Rafael Benitez ya ce dan wasan yanzu yana kan ganiyar sa. Kocin kungiyar Atletico Madrid Diego Simeone ya ce doke kungiyar Arsenal a gasar Europe shine zai kara ba da dama ga dan wasanta Antonie Griezmann 27, ya cigaba da zama a kungiyar ya kuma manta da batun komawarsa Barcelona.

Everton tana bukatar sayen matashin dan wasan tsakiya ba Nantes mai suna Kamal Bafounta. Kungiyoyi irinsu Inter Milan da Sevilla sun nuna sha'awarsu kan matashin danwasan mai shekaru 16.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Kungiyoyi Sun Fara Ruguguwar Dauko Layvin Kurzawa