Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Hada-Hada Da Musayar Zaratan 'Yan Wasa Na Ci Gaba Da Kadawa


Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce zai sayi dan wasan tsakiya dan kasar Brazil Fred wadda yake taka leda a kungiyar Shakhtar Donestk domin ya maye masa gurbin Paul Pgoba itama Manchester City ta nuna sha'awar na ganin ta sayo danwasan mai shekaru 24.

Ita kuwa Real Madrid tana da ra'ayin dauko Paul Pgoba daga Manchester United sai dai shugaban kungiyar ta Real Madrid Florentino Perez ya ce ba zai dauko dan wasan ba har sai ya rage albashi da yake bukata kuma ya nuna kwazonsa a gasar cin kofin duniya da za'ayi na 2018.

Manchester City tana bukatar dauko matashin dan wasan PSG Kylian Mbappe, 19, da kuma dan wasan tsakiya na Bayern Munich Thiago Alcantara 27 a karshen kakar shekarar nan.

Borussia Dortmund ta na bukatar zaman Michy Batshuayi, na din-din-din a kungiyar mai makon zaman aro da yake yi a wajanta inda ta dauko shi daga kungiyar Chelsea, Sai dai Chelsea tana bukatar kudi har fam miliyan £50 kafin ta amince da cinikin

Har Ila yau Chelsea tana da sha'awar dauko dan wasan tsakiya na Nice Jean Michael Seri akan kudi fam miliyan £35

Dan wasan baya na Manchester united Luke Shaw ya ce har yanzu bai yanke shawarar ko zai cigaba da zama a kungiyar ta Manchester ba sakamakon basu da kyakyawar alaka da mai horas da kungiyar José Mourinho.

Barcelona ta ware fam miliyan £60 wajan sayen dan wasan gaba na Manchester united Anthony Martial, 22, da kuma Ryan Sessegnon, 17, daga kungiyar Fulham. Liverpool da Tottenham sun tura tawagar su don sanya ido kan dan wasan gefe na kungiyar Benfica maisuna Andrija Zivkovic.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG