Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Uefa Na Tuhumar Pep Guardiola Da Kungiyar Liverpool


Hukumar kula da wasan kwallon Kafa ta nahiyar turai Uefa tana tuhumar Kocin Manchester, City Pep Guardiola, bisa zargin sa da rashin adalci da ya zargi alkalin wasan da ya hura wasansu da Liverpool a gasar cin kofin zakarun turai wadda aka yi a matakin wasan kusa da na kusa dana karshe a ranar larabara da ta gabata, inda aka doke Manchester City, da kwallaye 2-1 a karawar su ta biyu, da alkalin wasan ya sallami Pep Guardiola daga cikin wajan zamansa a filin wasan.

Mataki na 69 na dokokin Uefa ya nuna cewa duk wani kocin da aka fitar dashi daga filin wasa zuwa sama to baya da damar aika wani sako ta kowane irin yanayi zuwa ga ‘yan wasa.

Haka kuma hukumar ta Uefa tana tuhumar kungiyar Liverpool bisa kunna wuta da jefa wasu abubuwa a filin wasan a ranar da aka yi wasan. Don haka hukumar ta ce zata yi zama ranar 31 na watan Mayu domin duba hukunci kan lamarin.

Kocin Manchester City, zai sabunta kwantirakinsa a kungiyar na tsawon shekara guda bayan ya kammala aikinsa na yanzu a kungiyar. Har ila yau Kocin na hangen ‘yan wasa har guda uku da yakamata ya saye su zuwa Manchester city, nan da shekara biyu inda ake ganin zai kashe kimanin fam miliyan 600 wajan sayen su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG