Hukumar kula da wasan kwallon Kafa ta nahiyar turai Uefa tana tuhumar Kocin Manchester City Pep Guardiola bisa zargin rashin adalci da ya zargi alkalin wasan da ya hura wasansu da Liverpool na gasar cin kofin zakarun turai wanda akayi a matakin wasan kusa da na kusa dana karshe a ranar larabara da ta wuce Inda aka doke Manchester City kwallaye 2-1 a karawar su ta biyu.
Wanda alkalin wasan ya sallami Pep Guardiola daga cikin wajan zamansa a filin wasan.
Mataki na 69 na dokokin Uefa ya nuna cewa duk wani kocin wanda aka fice dashi daga filin wasa zuwa sama to baya da damar aika wani sako na kowane irin yanayi zuwa ga ‘yan wasa.
Haka kuma hukumar ta Uefa tana tuhumar kungiyar Liverpool bisa kunna wuta da jefa wasu abubuwa a filin wasan aranar da aka yi wasan. Don haka hukumar ta ce zata yi zama ranar 31 Mayu domin duba hukuncin kan lamarin.
Kocin Manchester City, zai sabunta kwantirakinsa a kungiyar ta tsawon shekara guda bayan ya kammala aikinsa na yanzu a kungiyar.
Har ila yau Kocin na hangen ‘yan wasa har guda uku da yakamata ya sayesu zuwa Manchester city, nan da shekara biyu inda ake ganin zai kashe kimanin fam miliyan 600 wajan sayensu.
Facebook Forum