Duk da dai ba a baiwa ‘yan kungiyar damar su gana da matan da aka samo sun yi gangamin murna da wasu daga cikin iyayen matan.
Ester Yakubu, na daga cikin iyayen da ‘yarta Dokas ke cikin wadanda aka sace, wadda ta ce ko cikin ‘yan matan 82 babu ‘yar ta to tana taya sauran uwaye murna. Kuma idan babu ‘yar ta yanzu gaba insha Allahu za ta ta zata fita.
Shi kuma, Yusuf Sallau, ya nuna godiya da jin dadinsa ga shugaban ‘kasa ga wannan alkawari da ya cika, da kuma taya murna ga iyayen yaran da za su sami ‘ya ‘yansu.
Da take amsa tambayar wakilin Muryar Amurka, kan cewa me yasa kungiyar bata yabawa kokarin gwamnati ganin yadda ake samo ‘yan matan, sakatariyar kungiyar BBOG, Aisha Yusufu, ta ce idan har gwamnati ba tayi abin yabo ba babu yadda za a yaba mata.
Kasancewar kungiyar ta yi tsayin daka kan ganin cewa an ci gaba da tashi tsaye wajen nemo ‘yan matan da aka sace.
Shugaba Buhari wanda ya dauki hoto da ‘yan matan 82 cikin farin ciki ya nufi Landon don ci gaba da duba lafiyarsa.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5