Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkar yada labarai Femi Adesina ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yanzu haka mataimakin shugaba kasa Prof. Yemi Osinbanjo zai ci gaba da tafiyar da alámuran kasar a matsayin mukaddashi.
A daren Lahadi (lokacin Najeriya) shugaba Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa Ingila.
Sanarwar da Adesina ya fitar ta nuna cewa tun da rana aka tsara Buhari zai kama hanyarsa ta London, amma aka jinkirta saboda tarbar ýan matan makarantar Chibok 82 da aka karbo daga hannun kungiyar Boko Haram.
Sanarwar ta kuma ce likitocin shugaban ne za su bayyana lokacin da ya kamata ya dawo daga wannan tafiya.
Sanarwar ta kuma nuna yadda Buhari ya mika godiyarsa ga ýan Najeriya bisa adduóin da suke masa na samun lafiya.
Tuni dai kamar yadda Adesina ya bayyana a sanarwar, Buhari ya aikewa da majalisar dokokin kasar da wasika kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.
A farkon watan Maris shugaba Buhari ya komo Najeriya bayan kwashe wani lokaci yana hutu tare da jinya a London.
Dama dai bayan dawowar shi gida, shugaban na Najeriya ya bayyana cewa mai yiwuwa zai sake komawa London domin ganin likitoci.