Wani rikici ya barke tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu kabilun Kuteb a karamar hukumar Ussa da kuma wani bangare na karamar hukumar Takum dake kudancin jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni daga jihar na cewa an samu hasarar rayuka da dama wasu kuma da dama sun samu raunuka kuma an kona dabbobin biyo bayan rikicin daya afku, tuni aka tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da abun ya faru,domin tabbatar da doka da oda.
Kawo yanzu akwai wasu makiyaya fiye da 150, da ba’a san inda suke ba,kamar yadda shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa reshen jihar Taraba Jauro Sahabi Mahmud Tukur ya bayyanawa manema labarai a Jalingo fadar gwamnatin jihar Taraba, inda ya bukaci hukumomin tsaro dasu kai musu dauki.
Haka zalika wani da ya ziyarci yankunan Bello Ahmadu Bela daga kungiyar Tabital Puulaku kira yayi ga gwamnatin jihar Taraba da ta hanzarta daukan matakin gaggawa ganin yadda lamarin ke neman kazancewa.
Kawo yanzu duk kokarin ji daga bakin shugaban karamar hukumar Ussan Rimamskwe Hassan Karma kan abubuwan dake faruwa ya ci tura domin ko da aka buga wayarsa ba’a dauka ba,an kuma aike masa da sakom karta kwanan kawo lokacin hada rahoto babu wani bayani daga gareshi.
A nasa bayanin da aka tuntube shi shugaban kungiyar cigaban al’umman Kuteb,Mallam Tanko Danjuma Kurmina yace ba haka zancen yake ba,inda yace su aka soma takala amma yanzu haka suna kokarin shawo kan lamarin.
Facebook Forum