Yayin da Fasaha ke ci gaba da rage girman duniya a idon mutane, ta hanyar kawo nesa kusa, haka kuma rinjayar da kafofin sadarwa ke yiwa mutane a bayyane yake. Babu maganar mutane nawa ne ke amfani da kafofin sadarwa, sai dai ace menene dalilan da yasa mutane ke amfani dasu.
A bayyane yake cewa yawancin mutane na amfani da hanyoyin ne domin kasancewa kusa da yan uwa da abokan arziki, har ma sanin abubuwan da ke faruwa a duniya. Wasu kuma na amfani da hanyoyin sadarwa ne domin daukaka kasuwancinsu.
Kadan daga cikin ire-iren hanyoyin sadarwa a wannan zamani sun hada da shafin Facebook da Whatsapp da Twitter da Palmchat da dai sauransu. Ga kadan daga cikin dalilan da yasa mutane ke amfani da wadannan shafuka.
Kasuwanci – mutane na amfani da hanyoyin sadarwa wajen saye da sayar da kayayyakinsu.
Shakatawa – wasu dayawa na amfani da kafofin sadarwa domin ta dauke musu kewa tare da rage musu lokaci.
Hulda da Jama’a – hanya ce mai baiwa mutane dama wajen hulda da mutane daban daban a fadin duniya.
Karatu – tabbas mutane na jin dadin karatu akan wayoyin hannu da kwamfuta fiye da yadda mutum zai bude littafi ya karanta.
Soyayya – dayawa mutane kan sami abokan rayuwarsu ta wannan sabuwar hanya.
Rayuwa cikin al’umma – mutane dayawa kan hadu a shafin sadarwa su kafa kungiya domin suyi tadi kan abinda suke so, missali masoya kwallon kafa ko dambe.
Labarai – hanyoyin sadarwa itace hanya mafi sauki da mutane suke samin labarai da dumi duminsu a wannan zamani.
Kirkira – tana baiwa mutane yanci da damar kirkirar duk abinda mutum yake so, missali mutum zai iya daukar sautin muryarsa ya kuma turawa duniya ta ji.
Sako cikin gaggawa – itace hanya mafi sauki da mutum zai aika da sako ko ina a fadin duniya sokon ya isa cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.