Wasu Amurkawa Sun Fara Jefa Kuri'unsu

Donald Trump da Joe Biden.

A yayin da zaben Amurka na ranar uku ga watan Nuwamba ke dada matsowa, masu kada kuri'a da dama na amfani da damarsu wajen jefa kuri’unsu da wuri da kansu ko ta hanyar akewa da sako, a jihohin da suka ba da damar yin haka.

A jihar Virginia, mazauna sun samu damar fara zabe tun a ranar 18 ga watan Satumba kuma akwai alamun kafa sabon tarihin yawan fitowar jama’a.

A wata cibiyar kada kuri’a a arewacin Virginia da ke wajen Washington, gundumar Colombia, jama’a sun soma fitowa tun da sanyin safiya, duk da cewa ranar zaben sauran kusan wata daya.

Layin sai karuwa yake yayin da rana ke dada budewa.

Kowa na sanye da takumkumin rufe fuska, kuma ana kiyaye ba da tazara. A kalla mintuna 45 ne tsawon locaci da ake jira a layi kafin jefa kuri'a.

“Banyi zaton haka ba, amma layin na ja fiye da yadda nake zato.. In da aiki yau amma wannan ya fi muhimmanci saboda haka zan hakura in yi,” a cewar Helen, wata mai jefa kuri'a a Virginia.

Fitowar jama’a a zaben na uku ga watan Nuwamba zai yi yawa sosai. A gundumar Fairfax shugaban zabe Gary Scott ya ce bai taba ganin layi mai tsawo a cikin shekaru 24 da ya yi yana aikin ba.