Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Sun Yi Musayar Zafafan Kalamai a Muhawararsu


Muhawarar Trump da Biden ta farko
Muhawarar Trump da Biden ta farko

An dai fara muhawarar ce cikin fara’a, wacce ta jirkice ta koma ta musayar kalamai kan batutuwan da aka tattauna akai.

Shugaban Amurka Donald Trump da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Joe Biden, sun yi musayar zafafan kalamai yayin da suka tafka muhawararsu ta farko kan manufofinsu.

Muhawarar ta wakana ne kasa da mako biyar gabanin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

An dai fara muhawarar ce cikin fara’a, wacce ta jirkice ta koma ta musayar kalamai kan batutuwan da aka tattauna akai, wadanda suka hada da annobar COVID-19, wacce ta halaka mutum miliyan daya a duniya, ta kuma yi sanadiyar mutuwar mutum sama da dubu 200 a Amurka.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Joe Biden ya ce “ shugaban ba shi da wani tsari. Bai kuma shimfida ko daya ba. Tun a watan Fabrairu ya san irin illar da ke tattare da cutar.”

Sai dai shugaba Trump ya ce, shi ko yake da tsari kan yaki da cutar.

Ya ce, “Muna da kayayyakin aiki kamar rigunan kariya, zuwa takunkumin rufe baki da hanci, mun kuma samar da na’urorin taimakawa numfashi, na san da ku ne da ba za ku samar ba, sannan makonnin kadan suka rage mana mu samar da allurar rigakafin cutar.”

Biden ya kuma caccaki Trump kan yunkurin da yake yi na ruguza tsarin inshorar lafiyan nan mai rahusa da ake kira Obamacare, wacce ke ba kusan mutum miliyan 20 damar samun inshorar lafiya.

Sai dai a cewar Trump, tsarin ya saba wa doka sannan ya takaita irin zabin da mutane ke da shi.

Amma Biden ya ce, masu kada kuri’a za su iya ci gaba da tsarin kiwon lafiyarsu a wani shiri da zai fitar wanda zai fadada tsarin na Obamacare.

“Za su iya a karkashin tsarina.” In ji Biden.

Nan da nan sai muhawara ta kaure, yayin da ‘yan takara biyu suka fara magana a lokaci guda.

“Tsarin kiwon lafiya na Obamacare ba shi da amfani, mu ne muka inganta shi.” In ji Trump.

Trump ya kuma zargi Biden da yunkurin samar da tsarin kiwon lafiya da za a rika amfani da kudaden gwamnati.

Wani abin takaddama yayin muhawarar shi ne, zabin da shugaba Trump ya yi na maye gurbin marigayiya Mai Shari’a Justice Ruth Bader Ginsburg, mai ra’ayin sauyi a kotun kolin Amurka. Trump ya zabi

Mai shari’a wacce ke da ra’ayin mazan jiya Amy Coney Barret, inda ya nemi a tabbatar mata da mukamin yayin da an riga an fara zabe a wasu jihohi da dama. Amma shi Biden gani yake, kamata ya yi a bari duk wanda ya lashe zaben watan Nuwamba ya zabi wanda maye gurbin Ginsburg.

Ya ce, “Amurkawa na da ikon su fadi ra’ayinsu kan wanda ya kamata a zaba a kotun kolin.”

Sai dai a na shi bangaren, Trump cewa ya yi, shi yake da hurumin ya fadi wanda ya kamata ya maye gurbin, ba tare da yin wani la’akkari da lokacin da ake ciki ba.

“Mu ne muka lashe zabe, saboda haka, mu ke da ikon mu zabe ta.”

Tim Murtaugh, Darektan sadarwa ne a gangamin yakin neman zaben shugaba Trump a wannan zabe na 2020.

Ya ce, “abin da masu kallon suka gani a wannan muhawara shi ne, shugaba Trump ya zama kwamanda a daukacin muhawara, kuma hakan ya fito da irin raunin da Joe yake da shi a mafi yawan lokacin da aka kwashe a muhawarar, wanda ya kwashe tsawon lokaci yana neman dauki daga mai jagorantar muhawarar.”

Sai dai wasu masu fashin baki sun soki yadda muhawarar ta gudana.

Jeremy Mayer, Malami a jami’ar George Mason, ya ce “a lokuta da dama, Biden zai yi magana ta dakika 10, 20, ko 30, sai kuma ka ga shugaban yana ta katse shi. Saboda haka, kusan babu ma’ana idan ka tambayi shin waye ya lashe muhawarar, saboda shugaban Amurka ya yi tsayi tsayin daka ya tabbatar cewa ba a yi muhawarar ba.”

To a halin yanzu dai, an kammala zagaye na farko kenan a muhawarar, amma kuma akwai wasu guda biyu da za a yi a watan Oktoba.

Ga Mahmud Lalo da cikakkiyar fassar ta sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG