Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yana Nan Kalau - Likitan Trump


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump da ya kamu da cutar COVID-19 ya aika sakon Twitter, yana mai nuna godiyarsa da kauna ga jama’a.

A daren jiya Trump ya wallafa cewa, “Ina ga komai na tafiya daidai! Ina mai godiya ga kowa da kowa,” inda ya kuma rubuta Kalmar “kauna” da manyan harufa a sakon nasa.

Wata takarda da Likitan shugaban na Amurka, Dr. Sean Conley ya aikawa Sakatariyar yada labarai a Fadar White House, Kayleigh McEnany a ranar Juma’a, ta ce, “ a wannan yammaci, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, shugaban na samun sauki.”

Ya kara da cewa, ba ya bukatar wata na’urar taimakawa numfashi, amma kuma bayan da muka tuntubi kwararru, mun zabi mu rika ba shi maganin Remdesivir.

A cewar Conley, Trump ya kammala zangon shan maganinsa na farko yana kuma samun kyakyawan hutu.”

Da tsakar ranar Juma’a aka kai Trump wani asibitin soji da ba shi da nisa da Fadar White House, inda ake sa ran zai kwashe wasu kwanani a wurin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG