Ganin cewa kokarin da hukumomi ke yi wajen shawo kan matsalolin rashin tsaro ba sa hana ‘yan bindiga yin aika-aikarsu ba, musamman a Arewa maso yammacin Najeriya, yanzu jama'a sun fara kosawa har sun fara tunkarar ‘yan bindigar da kan su.
Karin bayani akan: Sokoto, Sanusi Abubakar, Nigeria, da Najeriya.
Irin wannan ne ya faru a garin Gidan Buwai da ke Sokoto inda ‘yan banga wadanda ke taimakawa jami'an tsaro suka yi musayar wuta da barayin shanu kuma suka kashe mutum shida daga cikinsu a cewar shugaban kungiyar ta 'yan banga.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar mana da aukuwar lamarin.
A dalilin irin wadannan matsalolin ne ya sa wasu al'ummomi a jihar suka yi taron addu’o’i don kai kukansu ga Allah ya kawo saukin wadannan musifu.
Mutanen sun shafa mako daya suna saukar Alkur'ani tare da wasu addu'o'i na musamman.
Yayin Wata tattaunawa da Muryar Amurka wasu daga cikin mutanen yankunan sun ce idan mutum ya yi iya kokarinsa amma ya gaza, to sai ya koma ga rokon Allah.
Wannan kira na su dama abu ne wanda tun tuni malaman Musulunci suka dade suna shawarar ‘yan Najeriya da a koma ga Allah domin neman mafita daga wadannan musifu.
Saurari rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5