Sai dai har yanzu ba a ga gomman dalibai da aka sace daga kwalejin horar da harkokin noma da lamurran da suka shafi gandun daji ta gwamnatin tarayyya dake garin Afaka na karamar hukumar Igabi ba.
Da safiyar ranar Juma’ah ne dakarun sojin suka kubutar da mutum 180 wanda akasarin su dalibai ne na makarantar horar da harkokin noma da lamurran da suka shafi gandun daji ta gwamnatin tarayyya.
Karin bayani akan: sojin Najeriya, jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai, Nigeria, da Najeriya.
Tarin ‘yan bindiga da ba'a iya tantance adadinsu ba, sun kai farmaki a kwalejin da misalin karfe 11 da 30 a jiya Alhamis tare da yin awon gaba da gomman dalibai.
‘Yan bindigan dai sun kutsa cikin makarantar ne bayan sun fasa katanga tare da shiga daya daga cikin ginin makarantar mai nisan mita 600 daga harabar shiga makaranta inda suka sace dalibai daga bisani.Ma’ikatar harkokin tsaron cikin gida ta jihar Kaduna ta sanar da runduna ta 1 ta sojin Najeriya, da kuma dakarun horar da hafsoshin sama, wadanda suka kai agaji makarantar nan take inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigan.
Dakarun dai sun yi nasarar kubutar da mutane 180 da suka hada da yaran makaranta mata 42, malamai 8, da kuma dalibai maza 130, saidai a halin yanzu ba bu masaniya kan inda dalibai da suka hada da maza da mata 30 su ke.
Wasu daga cikin daliban da dakarun sojin sama da na kasa suka kubutar suna samun kulawa a asibitin soji sakamakon rauni da suka ji.
Bayan samun rahoto a kan cigaba da aka samu, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar ya yaba da kokarin dakarun na kai dauki cikin gaggawa da ya kai ga kubutar da mutane 180, tare da yin addu’ar Allah ya ba wa daliban da suka ji rauni lafiya.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, Tawagar hadin gwiwa da suka hada da sojojin sama da na kasa, Jam’ian ‘yan sanda da kuma jami’an tsaro na aiki tukuru wajen dawo da daliban da suke hannun ‘yan bindigan cikin koshin lafiya.