Wani Hadimin Shugaba Trump Ya Sake Amsa Laifi A Binciken Katsalandan Din Rasha

  • Ibrahim Garba

Mai bincike na musamman Robert Mueller

Baya ga wasu hadiman Shugaba Donald Trump da su ka mika kai ga mai bincike na musamman Robert Mueller, an sake samun wani hadimin Shugaba Trump da ya amsa laifi.

Yayin da su ke fuskantar karin matsin lamba daga mai bincike na musamman Rober Mueller, tsohon Shugaban kwamitin yakin neman zaben Trump Paul Manafort da kuma wani tsohon hadimin Trump Rick Gates, sun dau mabambantan matakai jiya Jumma’a, inda Gates ya amsa cewa ya aikata rashin daidai har sau biyu shi kuma Manafort ke fuskantar karin tuhumce-tuhumce a binciken da ake yi game da katsalandin din Rasha a zaben Amurka.

Gates, dan shekaru 45 da haihuwa, ya gurfana gaban kotun tarayya a Birnin Washington DC, don ya amsa laifi a masa rangwame kan zargin hada baki a cuci Amurka, da kuma zargin shata karya ga Hukumar Bincike ta FBI da mai bincike na musamman ranar 1 ga watan Fabrairu, yayin tattaunawar yarjajjeniyar amsa laifinsa a ofishin mai bincike, Mueller

A matsayin wani bangare na wannan yarjajjeniyar ta amsa laifi, Gates zai bai wa mai bincike na musamman Mueller hadin kai a binciken da Mueller ke yi kan ko shin kwamitin yakin neman zaben Trump ya hada baki da Rasha.