Kasar Sin za ta jaddada jagorancin da jam'iyyar Kwaminis ke bayarwa a kamfanin hada hadar kudinta mai kadarorin da suka kai dala tiriliya $61T, da kuma karfafa kokarinta na rage yawan basussukan cikin gida, kamar yadda kafafan yada labaran kasar suka rawaito, muhimmin taron manufofin kudi, inda suka ambato wani muhimmin taron da ake sau biyu cikin shekaru 10 wanda aka gudanar tsakanin 30 zuwa 31 ga watan Oktoba.
Babban taron harkokin kudi na tsakiya da aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin ya rawaito cewa, kasar Sin za ta tabbatar da hadin kan shugbancin jam’iyyar Kwaminisanci kan harkokin kudi.
Taron, wanda ya samu halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping da Firemiya Li Qiang, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta samar da wata hanya ta warware matsalolin basussukan cikin gida da kuma kula da basussukan kananan hukumomi.