Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan China Na Rububin Tikitin Balaguro Bayan Sassauta Matakan Corona


A China, ‘yan kasar wadanda suka kasance tamkar saniyar ware daga sauran kasashen duniya na tsawon shekara uku sakamakon tsauraran matakan yaki da coronavirus da gwamnatin kasar ta dauka, yanzu haka suna tururuwar siyan tikitin tafiye-tafiye, gabanin bude iyakokin kasar a wata mai kamawa.

WASHINGTON, D.C. - Hakan kuwa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar ta coronavirus a kasar.

Tsauraran matakan yaki da coronavirus da China ta dauka tun a 2020 – kama daga kulle iyakokin kasar, zuwa yawan sanya matakan kulle – sun tunzura jama’ar kasar a watan jiya nuna babbar adawarsu a fili a karon farko tun bayan da Xi Jingping ya zama shugaban kasar a 2012.

Yanzu da shugaba Xi ya sauya matsaya kwatsam a game da matakan kulle a kasar, matakan da suka yi mummunan tasiri akan tattalin arzikin kasar, cutar ta coronavirus ta na ci gaba da yaduwa sosai a kasar mai mutane biliyan daya da dubu dari hudu.

Sai dai alkaluma hukuma, sun nuna mutun guda ne kawai yam utu sakamakon cutar a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, abin da ya haifar da shakku a tsakanin masana a fannin kiwon lafiya da kuma ‘yan kasar a game da alkaluman.

Likitoci sun ce asibitoci sun cika makil da marasa ;afiya, akasarinsu, tsofaffi.

Masana kiwon lafiya na kasa da kasa sun yi kiyasin cewa miliyoyin mutane da ke kamuwa da cutar a kowacce rana, za isa a samu mutane miliyan daya da za su mutu sakamakon cutar a badi.

Daga cikin sassauta matakan, China za ta daina bukatar matafiya dake shiga kasar su killace kansu daga ranar takwas ga watan Janairu.

Hukmar shigi-da ficen China ta ce za ta dawo da yiwa ‘yan kasar passport, wadanda suke son yin balaguro zuwa wasu kasashe, sannan za ta dawo da amincewa da bukatun masu son kai ziyara Hong Kong.

Darajar Hannayen jarin wasu kamfanoni ta tashi, bayan da Chinan ta sanar da sassauta matakan yaki da cutar ta coronavirus.

Saurari cikakken rahoto daga Haruna Shehu Marabar Jos:

 ‘Yan China Na Rububin Tikitin Balaguro Bayan Sassauta Matakan Corona.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:40 0:00

XS
SM
MD
LG