Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Sojojin Ruwan China A Najeriya Wata Dama Ce Ta Magance Matsalolin Tsaro - Masana


Jiragen ruwan yaki uku na jiragen ruwan kasar China sun isa Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya,
Jiragen ruwan yaki uku na jiragen ruwan kasar China sun isa Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya,

Rundunar sojojin ruwan kasar China na yin wata ziyarar aiki a Najeriya cikin wannan makon, a wata ziyara da ba a saba gani ba a yammacin Afirka, inda China ke neman fadada tasirinta.

Jiragen ruwan yaki uku na jiragen ruwan kasar China sun isa Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya, a ranar Lahadin da ta gabata, dauke da sojojin ruwa kimanin 700.

A ranar Litinin rundunar sojojin ruwan Najeriya da ofishin jakadancin kasar China sun bayyana cewa, ziyarar ta kwanaki 5 na nuni da samun bunkasuwar dangantakar dake tsakanin China da Afirka, da nufin tinkarar matsalar tsaron teku, da tabbatar da kwanciyar hankali a mashigin tekun Guinea.

Jiragen ruwan yaki uku na jiragen ruwan kasar China sun isa Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya,
Jiragen ruwan yaki uku na jiragen ruwan kasar China sun isa Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya,

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro Chidi Omeje ya ce abin farin ciki ne kuma wata dama ce ga Najeriya da Afirka wajen magance matsalolin tsaro.

"Yana da mahimmanci cewa Najeriya ta ci gaba da rike irin wannan dangantaka saboda ba za mu iya tsayawa kan alakar kasashen yamma kadai ba, dole ne mu kara kaimi. China ta kasance babbar abokiyar hulda da Najeriya, muna bukatar mu’ammula da dukkan kamfanonin da za mu iya samu don samun damar tunkarar kalubalen tsaro daban-daban a fadin kasarmu da kuma yankin baki daya,” inji Omeje.

Rundunar sojojin ruwan kasar China ta kawo ziyarar aiki Najeriya
Rundunar sojojin ruwan kasar China ta kawo ziyarar aiki Najeriya

China ta dade tana zuba jari sosai a fannin samar da ababen more rayuwa a Afirka ciki har da Najeriya, tsawon shekaru da dama, kuma Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke samar da danyen mai na kasar China.

Sai dai ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa China na neman kafa sansanin sojin ruwa a mashigin tekun Guinea.

A bara, jami'an tsaron Amurka sun ce sun damu cewa irin wannan sansanin na iya yin barazana ga tsaron kasar Amurka.

Kabiru Adamu, wani manazarci a kamfanin Beacon tsaro mai kula da hadari, ya yarda cewa akwai yiyuwar ziyarar na da wasu bukatu da ba a bayyana ba.

A shekarar 2016, China ta yi alkawarin ba da tallafin tattalin arziki ga Sao Tome, wata karamar kasa ta Afirka da ke gabar tekun Atlantika, jim kadan bayan ta yanke hulda da Taiwan.

Sao Tome tana tsakiyar mashigin tekun Guinea ne, lamarin da ya sa ta zama cibiyar samar da mai da iskar gas.

Adamu ya ce China na kokarin tabbatar da kadarorinta a Afirka tare da yuwuwar samar da gidin zama na din-din-din.

"China tana da sha'awar fadada tasirinta a Afirka don kare kadarorinta, ta ba da jari mai yawa a kasashen Afirka kafin zuwan annobar COVID-19, da kuma lokacin annobar da kuma bayan ta. Tabbas za ta so ta kare wadannan jarin da kuma daya daga cikin hanyoyin da za ta iya yi shina karfafa alakar tsaro da kasashen Afirka,” inji Adamu.

A watan Janairu ne Najeriya ta bude tashar ruwa ta Lekki wato Deep Sea a Legas, wanda kamfanin kasar China Harbor Engineering Company ne ya gina.

XS
SM
MD
LG