Wani babban shugaban 'yan kabilar Igbo a yankin arewacin Najeriya ya shawarci 'yan kasar da su ci gaba da zaman lumana da juna, yana mai yin watsi da masu neman wargaza kasar ko neman tayar da fitina a tsakanin kabilunta.
Mazi Dominic Uzu, ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ne ke zuga matasa su na tayar da fitina a yunkurinsu na cimma wasu gurorin siyasar da suke ganin ba zasu iya cimmawa ba idan hankula su na kwance.
Shugaban na 'yan kabilar Igbo a Kaduna, wanda ya shafe shekaru fiye da 39 yana zaune a arewa, yace Arewa da dukkan al'ummarta 'yan'uwa ne a gare shi, kuma gida ne yankin a wurinsa, har ma yayi misali da wasu Hausawa abokansa wadanda mahaifinsa ya ba su fili suka yi gida, suka kuma yi iyali a yankin Igbo, kuma har yanzu su na zaune a can.
Saurari hirar Mazi Dominic Uzu a sama a gefen dama.