Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu yan bindiga su kaiwa wani ofishin 'yan sanda hari a Kano


Wata mace take juyayin mutuwar mijinta a irin hare haren da yan kungiyar Boko Haram suka kai.
Wata mace take juyayin mutuwar mijinta a irin hare haren da yan kungiyar Boko Haram suka kai.

Wasu 'yan bindiga, wadanda ake kyautata zaton yan kungiyar Boko Haram ne, su kai hari wani ofishin yan Sanda a Kano, arewacin Nigeria.

Tarzoma ta sake kunno kai a arewacin Nigeria a jiya litinin, lokanda wasu yan bindiga wadanda ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari wani ofishin yan sanda a Kano.

Wani jami'i yan sanda mai suna Ibrahim Idris ya tabbatar da harin amma bai bada wani karin haske ba.

Haka ma a jiya litinin akai hari kasuwar Gomboru a Maiduguri dake gabashin Kano. Ba'a dai bada rahoton ko wani ya jikkata ba a dukkan hare haren ba.

A watan jiya, yan yaki sa kan kungiyar Boko Harama suka kai hari Kano, harma aka kashe akalla mutane dari da tamani da biyar. Bayan wannan harin ne hukumomi suka kafa dokar hana fita.

An ga karin hare haren 'yan kungiyar Boko Haram cikin watani uku da suka shige, inda galibi suke auna ofisoshin 'yan sanda. Ita dai kungiyar tana so ne ta kafa amfani da shari'ar Musulunci a yawancin jihohin arewacin kasar.

Nigeria ita tafi kowace kasar Afrika yawan jama'a a yayinda take da kimamin mutane miliya dari da sitin kuma Musulmi ne suka fi yawa.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci a wasu yankunan arewacin kasar, inda aka yin tarzoma.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG