Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashe-fashe sun auku a wani birnin yankin tsakiyar Nijeriya


Wata motar bus din da fashewar ta rutsa da ita
Wata motar bus din da fashewar ta rutsa da ita

Shaidu sun ce wasu fashe-fashe biyu sun bararraka birnin Kaduna da ke

Shaidu sun ce wasu fashe-fashe biyu sun bararraka birnin Kaduna da ke yankin tsakiyar Nijeriya a yau dinnan Talata, ciki har da wani da aka kai daura da wata cibiyar soji.

‘Yan sanda sun ce daya fashewar ta auku ne a kusa da wata gada a sa’ilinda dayar kuma ta auku a kasar ginin hedikwatar bataliya ta daya (1st Div) da ke gefen garin Kaduna. Hukumomi sun ce abin ya rutsa da wasu.

‘Yan sanda na binciken bayanin da ke nuna cewa wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin na cibiyar soji bayan da ya sheko a guje da mota ya doki kofar shiga. Shaidu sun ce sojoji sun killace wurin sun kuma hana masu ayyukan ceto kai wa wurin.

Babu wanda ya dau alhalin kai harin nan da nan. Tsattsaurar kungiyar nan ta Islama mai suna Boko Haram, ita kan kai munanan hare-hare kan ‘yan sanda, soji da kuma cibiyoyin gwamnati.

Kaduna na da tazarar kilomita 200 kudu da Kano, inda ‘yan Boko Haram su ka dau alhakin kai jerin hare-haren da su ka yi sanadin hallaka mutane 180 a watan jiya.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG