Wani Mutum Ya Daba Wa Shugaban 'Yan Adawar Koriya Ta Kudu Wuka A Wajen Wani Taro

Shugaban ‘Yan Adawar Korea Ta Kudu Lee Jae-myung

An caka wa shugaban jam'iyyar adawa ta Democratic a Koriya ta Kudu wuka a wuya, yayin wata ziyara da ya kai birnin Busan da ke kudancin kasar yau Talata, aka kuma dauke shi a jirgin sama zuwa wani asibitin Jami’a domin yi mashi jinya bisa ga cewar Jami'an jam'iyyar da na kashe gobara.

WASHINGTON, D. C. - Wani mutum da ba a tantance ba, ya kaiwa Lee, wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekarar 2022 hari a lokacin da yake rangadin wurin wani filin da ake shirin gina tashar jirgin sama, kamar yadda jami'ai suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

An dauki Lee da wani jirgin sama mai saukar ungulu na sashen kashe gobara, zuwa asibitin jami'ar Pusan inda ake jinyarsa a dakin jinyar masu bukatar kula ta gaggawa, kamar yadda wani jami'in asibiti da jami'in kashe gobara suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Lee Jae-myung lokacin da wani mutum da daba masa wuka, a Busan, Janairu. 2, 2024.

Maharin ya yi kama da mai shekaru 50 zuwa 60, wanda ya sanya rawanin takarda mai sunan Lee, kamar yadda aka nuna a hotunan kafofin watsa labarai.

Mutumin ya matso kusa inda ya nemi Lee ya sa mishi hannu a wani littafi lokacin da Lee ke magana a tsakanin magoya bayansa da ‘yan jarida, sannan mutumin ya yi gaba ya kai masa hari, kamar yadda faifan bidiyo suka nuna.

Hotunan sun nuna, wasu mutane da suka hada da ‘yan sanda suka damke maharin nan da nan.

Shugaban kasar Yoon Suk Yeol ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa, wannan wani abu ne da ba za a lamunta ba, in ji ofishinsa. Ya nuna matukar damuwa da halin da Lee ya shiga, ya kuma ba da umarnin a ba shi kulawa ta musamman yadda zai samu murmurewa cikin gaggawa, in ji ofishin sa.

-Reuters