Salman Rushdie, marubucin nan wanda wani rubutu da ya yi ya janyo masa barazanar hukuncin kisa daga Iran a shekarun 1980, yau Jumma'a wani mutum ya kai masa hari a wani dandalin taro yayin da yake shirin gabatar da lacca a yammacin New York, kuma da alamar maharin ya caka masa wuka a wuya.
Wani dan jaridan kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya shaidi yadda wani mutum da ya tinkari Rushdie a kan mumbarin a cibiyar Chautauqua, ya shiga naushinsa ko daba masa wuka sau 10 zuwa 15 yayin da ake gabatar da shi. An tura marubucin mai shekaru 75 ya fadi a kasa, kuma an kama mutumin.
Musulmi da dama na daukar Littafinsa na 1988 mai suna "Ayoyin Shaidan" a matsayin sabo. Zanga-zangar adawa da rubutun na Rushdie mai yawan gaske ta barke a duniya, ciki har da tarzomar da ta kai ga mutuwar mutane 12 a Mumbai.
An haramta littafin a Iran, inda marigayi Ayatollah Ruhollah Khomeini ya ba da fatawa, ko kuma doka a 1989, yana kira da a kashe Rushdie.