Wani Mummunan Hari Da Isra'ila Ta Kai Gaza Ya Kashe ‘Ya’yan Shugaban Hamas Uku Da Jikokinsa Hudu

Israel-Hamas

Jiragen saman Isra'ila sun kashe 'ya'yan babban jagoran siyasar Hamas guda uku a zirin Gaza a jiya Laraba, a daidai lokacin da Isra'ila ke gudanar da tattaunawar tsagaita bude wuta da kungiyar ta Hamas.

WASHINGTON, D. C. - Kungiyar Hamas ta ce an kuma kashe jikokin shugaban hudu.

Isma’il yace “Ya'yan Ismail Haniyeh shugaban Hamas, na daga cikin manyan mutane da aka kashe a yakin ya zuwa yanzu. Isra'ila ta ce su ma yaran 'yan Hamas ne, ya kuma Isra'ila da kai wannan hari cikin "niyyar daukar fansa ne da kisa."

Mutuwar dai ta yi barazanar kawo cikas ga shawarwarin tsagaita bude wuta da kasashen duniya suka shiga, wanda ake ganin ya yi kamari a 'yan kwanakin nan duk da cewa bangarorin sun yi nisa kan muhimman batutuwa.

Iyakar Israel-Gaza, April 10, 2024.

Kisan ya kuma zo ne a daidai lokacin da Isra'ila ke kara fuskantar matsin lamba daga babbar kawarta, Amurka, na sauya salon yaki, musamman ma batun taimakon jin kai ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali a Gaza.